Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, ya bayyana cewa jam’iyyarsa za ta yi aiki tukuru domin tabbatar da cewa jam’iyyar APC mai mulki ba za ta samu sama da kuri’u 15,000 ba a Jihar Kano a zaben 2027.
Tsohon gwamnan jihar ya ce jam’iyyarsa za ta yi duk mai yiwuwa domin rage karfin APC, kamar yadda suka sanya jam’iyyar PDP ta samu kasa da kuri’u 15,000 a zaben 2023.
Kwankwaso ya yi wannan jawabi ne yayin da yake karbar bakuncin tawagar NNPP daga yankin Kano ta Arewa a gidansa da ke Miller Road a Kano.
Ya yaba wa kokarin jam’iyyar a zaben 2023, inda suka yi nasarar rage karfin PDP duk da cewa NNPP sabuwar jam’iyya ce wadda ta fara yakin neman zabenta da makare.
Ya ce lokaci ya yi da za su rage tasirin APC a jihar, yana mai kira ga magoya baya da su kara kaimi wajen gangamin matakin karkara domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a gaba.
Shugaban tawagar wakilan, Abdul Bichi, ya bayyana wa manema labarai cewa sun je ziyarar domin tabbatar da biyayyarsu ga jagoran jam’iyya na kasa, Kwankwaso, tare da nisantar tsohon Sakataren Gwamnati (SSG), Dr. Abdullahi Baffa Bichi.
Abdul ya ce: “Mun raba gari da tsohon SSG tun bayan cire shi daga mukaminsa. Mun zo nan ne domin tabbatar da biyayyar mu ga Kwankwaso da jam’iyyar NNPP, kuma ba za mu bar jam’iyyar ba, ba za mu bi tsohon SSG ba.”
A baya an zargi tsohon SSG, Dr. Baffa Bichi, da kafa wani rukunin da ke goyon bayan Gwamna Abba Yusuf domin karbar ragamar gwamnati daga Kwankwaso (tsaya da kafarka) , lamarin da ya haifar da dakatar da shi daga jam’iyyar a jihar, sannan daga bisani ya rasa mukaminsa na SSG, duk da cewa gwamnati ta danganta cirewar da matsalolin lafiya.