Majalisar Dattijai ta bada umarnin kama darektan gudanarwa na kamfanin gine gine na Julius Berger, Dr. Peer Lubasch, saboda kin halartar ganawar kwamitin Ayyuka na Majalisar.
Wannan shawara ta biyo bayan korafin da Sanata Osita Ngwu (PDP, Enugu West), ya gabatar a yau Alhamis a zauren majalisar.
Sanata Asuquo Ekpenyong daga Cross River da Sanata Mpigi Barinada daga Rivers ne suka goyi bayan korafin da Sanata Ngwu ya gabatar inda yace kamfanin Julius Berger Nigeria Plc ya ki girmama gayyatar kwamitin Majalisar Dattijai kan Ayyuka a lokuta da dama.
Kwamitin ya nemi karin bayani kan yadda akayi watsi da aikin da kuma yadda aka kudin kudin kwangila daga Naira biliyan 54 zuwa Naira biliyan 195.
A cewar Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio, za a bayyana rana ta musamman domin tilasta halartar Dr. Lubasch bayyana gaban kwamitin Ayyuka na Majalisar.