Tsohon Senatan da ya wakilci Yankin Kaduna Tsakiya, Shehu Sani, ya soki kalaman da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, yayi game da mayarda martani a aure.
A tuna cewa Sanusi ya ba ‘ya’yansa shawara da su mayar da martani idan mazajensu sun buge su, wani magana da yayi a lokacin taron Tattaunawar Kasa kan cin zarafin Jinsi (GBV) a Jami’ar Bayero, Kano
A cikin martani da yayi a shafinsa na Facebook, Sani ya bayyana kin amincewa da tallata kawo ramuwar gayya ta hanyar tashin hankali, yana mai jaddada cewa hakan na iya lalata aure.
“Mai Martaba Sanusi bai kamata ya karfafa irin wannan ba, ta hanyar bugu da mayar da martani. Maimakon haka, maza da mata su koyi yadda za su kula da kansu a lokacin fushin,” ya rubuta.
Tsohon senatan ya bayyana cewa warware rikice-rikice cikin lumana shi ne mafita mai ɗorewa.
“Idan mijin yana fushi, ya kamata ya fita daga gidan sannan ya dawo daga baya. Idan mijin yana jin haushi yana ihu, matar tayi shuru kawai ta bar shi ya fitar da dukkan maganganunsa.”
“Kalmar ‘A yi haƙuri’ tana da ƙarfi a cikin gida,” ya kara da cewa.
Ya yi gargadi cewa, “Ranar da buga juna da mayar da martani ya zama al’ada a cikin gida, aure zai lalace ba tare da wani gyara ba, ko da kuwa ma’auratan suna ci gaba da zama tare.”