Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya amince da biyan kyautar albashin wata guda ga ma’aikatan gwamnati da na hukumomi a jihar.
Wannan amincewar ta fito ne a wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan Jihar ya fitar a ranar 28 ga Disamba, 2024.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan albashi shi ne karo na biyu a tarihin jihar, wanda aka fara biya a mulkin Gwamna Lawal a shekarar 2023.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Suleiman Idris, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce ma’aikata da masu ritaya za su karɓi ƙarin 30% na albashinsu na asali a matsayin albashin wata ta 13.
“Wannan tsari na nufin nuna godiya ga sadaukarwa da ƙoƙarin ma’aikatan Zamfara ta hanyar samar musu da ƙarin tallafi na kuɗi yayin lokacin bukukuwan karshen shekara.
“Biyan albashin wata ta 13 na daga cikin manufofi da dama da ake aiwatarwa don karfafa ma’aikata da bunkasa tattalin arzikin Jihar Zamfara.
“Domin cika alkawuranta, gwamnatin ta biya bashin fansho sama da Naira biliyan 10 da aka tara tsawon shekaru 11, ta amince da mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, tare da tabbatar da cewa an biya albashin ma’aikata akan lokaci,”in ji Idris.