Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane biyu, Ado Ahmad mai shekaru 35 dake unguwar T/murtala da wani dan uwansa, da laifin zuba wani ruwan rubuta a wata rijiya.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa yace kiran da suka samu daga garin Durmawa a karamar hukumar Bebeji ne ya sanya suka tura jami’ai don cafke wadanda ake zargin.
Sai dai wanda aka kam yace rubutun neman sa’ar kasuwa ne, ba wani abun cutar da jama’a ba.
Sanarwar da kakakin ya fitar a yammacin Alhamis tace kawo yanzu dai rundunar na cigaba da bincike kan lamarin.