Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Joe Igbokwe, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, shine ya kafa tubali mai karfi wanda Shugaba Bola Tinubu zai ci gaba da ginawa a kai.
Igbokwe ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da maganganun da ke cewa Buhari ya gaza, yana mai cewa alamomin nasarorinsa sun bayyana ga kowa.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, Igbokwe ya ce:
“Kada wani mai rai ko matacce ya yarda da tunanin cewa Buhari ya gaza. A daina wannan tunanin.
“Ya kafa tubali mai karfi wanda Tinubu ke ginawa a kai. Muna ganin alamomi da nasarorinsa a yau.”
Maganganun Igbokwe sun biyo bayan wata kalamai daga tsohon Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Siyasa, Babafemi Ojudu, wanda ya ce Buhari ba shi da hangen nesa.
Ojudu ya bayyana cewa rashin hangen nesan Buhari ya sanya bai goyi bayan takarar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, don zama shugaban kasa ba.