Mataimakin gwamnan jihar Borno, Dr. Umar Kadafur da wasu fasinjoji 100 sun tsallake rijiya da baya bayan injin jirgin da s uke ciki yak ama da wuta.
Jirgin Max Air ya dauko fasinjojin daga jihar Borno zai kai su birnin Abuj da misalin 7:00 na yammacin Laraba, amma da tashinsa, sai injinsa ya kama da wuta.
Hatsarin ya zo da sauki bayan direban jirgin ya yi nasarar juya akalarsa, kuma ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Maiduguri a jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya buge wani tsuntsu a lokacin da ya tashi, wanda haka ne ya sa injinsa yak ama da wuta.
Wani ma’aikacin kamfanin Max Air, daya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da afkuwar lamarin da safiyar yau Alhamis.
Sai dai, nan take hukumar gudanarwar Max Air ta tura wani jirgin saman daga Kano domin yin jigilar fasinjojin, ciki harda mataimakin gwamnan zuwa Abuja.