Majalisar Gwamnonin Arewa Maso Gabas ta yi ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, kan rasuwar mahaifiyarsa, Maryam Namadi, da babban ɗansa, Abdulwahab Namadi.
Wannan sanarwa ta fito daga bakin Shugaban Majalisar Gwamnonin Arewa Maso Gabas da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum.
Sanarwar ta fito ta bakin mai magana da yawun Zulum, Dauda Illiya, a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce: “A madadin al’ummar Jihar Borno da kuma dukkanin yankin Arewa Maso Gabas, ina mika ta’aziyyata mai zurfi ga His Excellency Namadi da al’ummar Jihar Jigawa kan wannan babban rashin mahaifiyar ku da ɗanku.”
Zulum ya yi addu’a Allah ya sanya su a Al-Jannatul Firdaus.
A tuna cewa dan Gwamnan, Abdulwahab, wanda yake da shekaru 24, ya rasu ne sakamakon haɗarin mota a hanyarsu ta dawowa daga Kafin Hausa tare da abokansa, kwana guda bayan rasuwar kakarsa, Hajiya Maryam.