Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya yafe wa fursunoni 11 a jihar a matsayin kyautar Sabuwar Shekara.
Gwamnan ya sanar da wannan hukunci a yayin da yake gabatar da jawabin Sabuwar Shekara a ranar Laraba a Jos, inda ya bayyana cewa wannan mataki ya dace da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi da kuma shawarwarin Majalisar Shawara ta Jihar Filato kan yafe wa wadanda aka hukunta.
“Ina amfani da ikon da aka ba ni a cikin Sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulki na 1999, kamar yadda aka gyara, kuma bayan tattaunawa da Majalisar Shawara ta Jihar Plateau kan yafe wa wadanda aka hukunta, na yanke shawarar yafe wa fursunoni 11.
Daya daga cikin ‘yan fursunan ya samu cikakken yafewa, yayin da gwamnati ta biya kudaden tara na wasu guda 10,” in ji Gwamna Mutfwang.
Ya kara da cewa an yi la’akari da fursunoni don yafe musu bisa la’akari da nadamar da suka nuna game da laifukan da suka aikata, wanda Majalisar Shawara ta tantance.