Kungiyar hadin kan addinai ta kasa ta kalubalanci gwamnati a dukkan matakai kan matsalar tsaron dake ci gaba da karuwa a kasar nan, tare da fatan bangarorin zasu gaggauta ganowa tare da hukunta mutanen da ke da alhakin taaddanci a kasar nan.
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta kasa, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN), Daniel Okoh, ne suka yi wannan kiran, yayin taron da suka gudanar a Abuja jiya Talata.
Sarkin Musulmi, wanda ya yi magana bayan shugaban Kiristocin ya kammala ya ce akwai bukatar yan Najeriya su koma ga Allah, tare da neman sauki a wajensa domin samun saukin rayuwa.
Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya kuma yabawa mambobin majalisar addinan da masu ruwa da tsaki, musamman sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, bisa jajircewar da suka yi na tabbatar da zaman lafiya a addinai a shekarar 2024.
Tun da fari, shugaban CAN, Okoh, ya bayyana cewa Najeriya na da dimbin albarkatun kasa wadanda ke da karfin samar da ci gaban kasa, samar da ayyukan yi, kawar da talauci, da inganta rayuwa ga daukacin yan Najeriya, a don haka ya bukaci shuggabanni akan su mayar da hankali kan yadda yan kasa zasu amfana da dimbin arzikin.