Shugaban Ƙasa Bola Tinubu tura sakon Kirisimeti ga kiristocin kasar nan, inda ya nemi su sa shugabannin Najeriya a cikin addu’o’insu
Shugaban ya ce su shugabanni suna buƙatar tare da goyon baya domin ƙasar ta ci gaba.
Tinubu ya bayyana haka ne a saƙonsa na Kirsimeti, inda ya taya al’uumar Najeriya murna.
Ya bukaci Kiristoci su yi amfani da ranar domin sabunta addu’o’i na cikar burinsu na samun ingantacciyar Najeriya.
Ya kuma yi kira ga ƴan ƙasar su tuna marasa ƙarfi, musamman maƙwabta da ƴan’uwa da abokai da sauran abokan hulɗa.
Sannan ya dauki alkawarin za su tabbatar da tsaro a hanyoyi domin ba masu tafiye-tafiye damar gudanar da zirga-zirgarsu lafiya.