Rahotanni sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin tare da wani abun fashewa da aka kera da hannu.
An kwato kayan fashewar, sannan an kama wanda ake zargin.
Dakarun hadin gwiwa na Multinational Joint Task Force (MNJTF), tare da hadin kan ‘yan sa kai na Civilian Joint Task Force (CJTF), sun kama wani wanda ake zargin mai kai kayan aiki ne ga ‘yan ta’adda a kofar shiga karamar hukumar Gubio a jihar Borno.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Sojoji, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya tabbatar da kama wanda ake zargin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumma’a, 3 ga Janairu, inda ya ce an kama shi a ranar Alhamis, 2 ga Janairu.
Sanarwar ta bayyana cewa:
“An kama wanda ake zargin mai suna Mukhtar Alhaji Chari, mai shekaru 28, yana kai kayan aiki zuwa garin Damasak, karamar hukumar Mobbar, domin kai hari akan dakarun MNJTF.”
“Abubuwan da aka gano sun haɗa da:
Silinda 12kg guda huɗu marasa komaiS, ilinda 6kg guda ɗaya mara komaiC, anister na carburetor guda biyu, mai sarrafa matsin iska guda biyu da kuma bututun roba.”
Rahotannin sirri sun nuna cewa an tsara amfani da kayan domin kai hari na ramuwar gayya bayan rasa mayaka da dama da kuma kwace manyan makamai daga hannunsu.
“Kama wannan mai kai kayan fashewa da kwato kayan aiki ya dakile yuwuwar kai hari na ta’addanci, tare da rage ƙarfin ayyukan ‘yan ta’adda.”
Wanda ake zargin yana hannun hukuma kuma yana taimakawa wajen bincike.
Kwamandan MNJTF, Manjo Janar Ibrahim Ali, ya yaba wa sojoji da CJTF bisa ga himmarsu da ƙwarewarsu, inda ya jaddada niyyar MNJTF na yaki da ta’addanci domin tabbatar da tsaro a yankin.