Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar ceto mutane 25 da yan bindiga su ka yi garkuwa da su a Kaduna bayan kashe yan bindiga uku.
Sojojin sun gudanar da aikin ceton a karkashin rundunar Safe Haven da aka yi a Kudancin Kaduna.
Yayin harin da su ka kai, an ci karo da wani karamin asibiti da ake jinyar yan bindiga da su ka ji rauni.
Dakarun sun kai samame yankunan Ruwan Sanye, Randa, Rafin Gora, Gari, Libera makaranta duk a karamar hukumar Kauru na jihar Kaduna.
Sojojin sun gudanar da aiki karkashin shirin Golden Peace domin ba manoma damar girbe amfanin gonakinsu, da tsaron rayuka gabanin bikin kirsimeti.