Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a a jam’iyyar LP, Peter Obi, ya na ganin gindaya sharuɗa kan tarukan raba tallafi na iya rage himma da sha’awar ƴan Najeriya da ƙungiyoyi wajen taimakon al’umma.
Peter Obi ya fadi hakan ne yayin martani kan kiran babban sufeto janar na ƴan sandan Najeriya, wanda ya bukaci ƙungiyoyi da mutane su riƙa sanar da ƴan sanda tare da bin dokokin shirya taruka kafin su raba tallafi.
Babban sufeton ƴan sandan ya bayyana wannan matakin ne saboda yawan turmutsutsun da ke faruwa a wuraren rabon tallafi, wanda a lokuta da dama ya yi sanadiyar asarar rayuka a ƙasar.
Sai dai Obi ya yi gargadi cewa irin wannan tsari zai iya rage kwarin gwiwa ga masu taimakon al’umma.
A wata hira da Channels TV, Obi ya ce: “Duk da cewa kashedin yana da mahimmanci, amma gindaya waɗannan sharuɗan na iya sa wasu su janye daga taimakon al’umma. Maimakon a buƙaci mutane su nemi izini kafin su taimaka, zai fi dacewa a ba su shawara su ɗauki matakan da za su hana faruwar turmutsutsu.”