Majalisar dokokin jihar Edo ta dakatar da dukkan zababbun shugabanni da mataimakan shugabannin kananan hukumomi 18 na jihar.
Majalisar ta bayyana daukar matakin ne bisa zargin su da almundahanar kudaden kananan hukumomi.
An yanke shawarar dakatarwar a yayin zaman majalisa na ranar Talata bayan zazzafar muhawara.
An umarci shugabannin sassan majalisar na kowace karamar hukuma da su jagoranci gudanar da ayyukan kananan hukumomin na tsawon wata biyu masu zuwa.