Asusun Tarayya ya samu ƙaruwa da 45% na kuɗaɗen shiga tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kama mulki.
Shugaban hukumar rarraba kuɗaɗe da daidaita alƙaluma ta ƙasa (RMAFC), Dr. Mohammed Bello Shehu ya fitar da bayanin haka.
Yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Talata, Dr. Shehu ya danganta wannan ci gaba da manufofi da sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta kawo.
Ya bayyana waɗannan sauye-sauye, ciki har da ƙudirin gyaran dokokin haraji, a matsayin matakan da za su sake fasalin tsarin samun kuɗaɗen shiga ga Najeriya da magance manyan matsalolin tattalin arziki.
Dr. Shehu ya amince da cewa yanayin tattalin arziki ya na cikin wani yanayi , wanda ke kawo wahala ga ’yan Najeriya a halin yanzu, amma ya ce akwai amfani masu yawa a nan gaba.
“Mun san akwai ƙalubale a ƙasar – wahalhalu da sauran su – amma a ƙarshe, waɗannan sauye-sauyen za su ɗaukaka Najeriya a cikin ƙasashen da ke samun ci gaba sosai. Tattalin arzikin ƙasa (GDP) zai ƙaru sosai,” in ji shi.