Kotun daukaka kara, mai zamanta a Abuja, ta soke hukuncin kotun da’ar ta ma’aikata wanda ya dakatar da shugaban hukumar kula da korafe-korafe da yaki da cin hanci ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji.
A zaman kotun da Mai Shari’a Umaru Fadawu ya jagoranta, ta amince da hujjojin lauya mai kare Magaji, Adeola Adedipe (SAN), cewa umarnin kotun da’ar ya nuna wariya kuma bai ba wanda yake karewa damar adalci ba.
Mai Shari’a Fadawu ya umarci a mayar da batun gaban wata kotun da’ar ta ma’aikata (CCT) ta daban.
DAILY POST ta ruwaito cewa a baya, wata kotun da’ar ma’aikata mai mutum uku, karkashin jagorancin Mai Shari’a Danladi Umar, a ranar 4 ga Afrilu, a Abuja, ta bayar da umarnin dakatar da Magaji daga mukaminsa.
Kotun ta ba da umarnin ne bisa zarge-zargen da hukumar da’ar ma’aikata ta gabatar kan Magaji.