Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ba da umarnin kama masu sayarwa da masu sayen kayan aikin noma da gwamnatin jihar ta bayar kyauta ga manoma.
Gwamnan ya ba da wannan umarni ne a Bagudo yayin kaddamar da raba kayan aikin noma da Muhammad Bello Ka’oje, wakilin mazabar Bagudo/Suru a Majalisar Wakilai, ya bayar kyauta ga manoma.
Gwamna Idris ya ce waɗanda suka karɓi kayan aikin noma kyauta su yi amfani da su wajen bunƙasa amfanin gonakinsu, musamman a harkar noman rani.
“Dole a yi amfani da kayan wajen noma, kada wani ya sayar da su don neman kuɗi a kowane dalili,” in ji gwamnan.
“An umurci jami’an tsaro su kama duk wanda aka samu yana sayarwa ko siyan kayan aikin noma da gwamnati ta bayar domin samar da abinci. Ba ku da hujjar sayar da kayan,” ya gargade su.
A nasa ɓangaren, Bello Ka’oje ya bayyana cewa mutane 9,400 daga ƙananan hukumomin Bagudo da Suru sun amfana da kayan aikin noma da tallafin sana’o’i.
“An raba injinan ban ruwa 180, buhunan iri na shinkafa mai inganci 550, buhunan iri na masara mai inganci 1,380, akwatunan feshi (sprayers) 2,000, da buhunan abincin dabbobi (dussa) 1,000 ga manoma da makiyaya Fulani,” in ji shi.
“Haka nan, an raba babura 50 da kekunan dinki 150 don taimaka wa masu cin gajiyar su dogara da kansu,” inji shi.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bagudo, Aliyu Sambo Zagga, ya gode wa Gwamna Nasir Idris saboda kokarin kafa tashar tsandauri ta Lolo Dry Port a yankin, domin bunƙasa cinikayya da tattalin arziki ga Jihar Kebbi da yankin Arewacin Najeriya baki ɗaya.
Ya bayyana cewa dukkan masu gonaki da aka kwace domin aikin sun karɓi diyya daga gwamnatin Kebbi, inda aka biya su diyya daga Naira miliyan ɗaya zuwa sama.