Kwanaki biyu kafin ƙarewar shekarar 2024, Gwamna Seyi Makinde ya cika alkawarin da ya yi na biyan ma’aikatan jihar Oyo Karin albashin wata guda.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Labarai da wayar da kan Jama’a, Prens Dotun Oyelade, ya fitar a ranar Talata, yace wannan ya zo ne duk da cewa gwamnatin jihar Oyo na kashe naira biliyan 77 kowacce shekara domin biyan albashinn ma’aikata da sauran kuɗaɗen aiki.
“Watanni biyu da suka gabata ne, Gwamna Makinde ya amince da biyan mafi ƙarancin albashi na naira 80,000 ga ma’aikatan gwamnati bayan an warware matsalar da ta shafi daidaita albashi a cikin kwamitin tattaunawa.
“Daga ranar 1 ga Janairu 2025, gwamnatin za ta rika biyan jimillar naira biliyan 143 a kowace shekara kan albashi, hakan ya faru ne bisa amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi. Wannan ya nuna ƙari mai yawa na kashi 86% a albashin da kuɗaɗen aiki,” a cewar Oyelade.
Ya kuma bayyana cewa wannan ya sanya jihar Oyo shiga cikin jihohin da ke da mafi girman albashin ma’aikata a ƙasa baki daya.
Ya ƙara da cewa jihar Oyo c eke da mafi yawan ma’aikatan gwamnati a kudu maso yammacin Najeriya.
A watan Disamba na shekarar 2023, Gwamna Makinde ya yi alkawarin biyan ma’aikatan gwamnatin jihar Oyo albashin wata 13 kafin ƙarshen sabuwar shekara.