Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sake aikewa da ƙarin sunan Nura Iro Ma’aji domin nada shi a matsayin kwamishina, wanda hakan ya zama kari akan mutane shida da aka aikewa majalisar dokokin kano a jiya Litinin.
Da yake karanta wasikar yau a zaman na yau, kakakin majalisar Jibrin Isma’il Falgore yace ƙarin kwamishinan ya biyo bayan amincewa tare da tantancewa domin naɗa shi a matsayin mamba a majalisar zartarwa.
A kwanakin baya gwamnan ya fara gudanar da sauye-sauye a gwamnatinsa inda ya sauke kwamishinoni biyar ya kuma chanjawa wasu ma’aikata.