Darajar Naira ta karu a kan Dala a kasuwannin canjin kuɗi na gwamnati da na bayan fage a ranar Alhamis.
Bayanai daga Babban Bankin kasa (CBN) ya nuna an canjar da Naira kan N1,532 kan Dala a ranar Alhamis, wanda ya gaza N1,545 da aka canjar da ita ranar Laraba.
A kasuwar bayan fage, Naira ta samu ƙaruwa, inda aka canjar da ita tsakanin N1,640 da N1,680 kan Dala a ranar Alhamis, idan aka kwatanta da N1,710 da aka samu a ranar Laraba,