Jami’ar Bayero da ke Kano ta sanar da daga matsayin Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo zuwa Farfesa a fannin Hadith.
Wannan na kunshe a wata sanarwa da jami’ar ta fitar a yammacin ranar Juma’a.
Shafin Facebook na Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya tabbatar da wannan cigaba, inda mabiyansa suka yi ta taya shi murna bisa wannan babban matsayi da ya samu.
Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo, wanda yanzu ya zama Farfesa, yana daga cikin fitattun malamai masu tasiri a harkar addinin Musulunci a Najeriya. Malamin ya shahara wajen koyar da tafsirin Al-Qur’ani mai girma da wa’azantarwa ga al’umma a ciki da wajen Najeriya.
A matsayinsa na malami a jami’ar Bayero, Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo yana koyarwa a sashen addinin Musulunci, inda yake ilmantar da dalibai tare da bayar da gudunmawa ga cigaban al’umma. Wannan sabon matsayi zai kara masa damar cigaba da taka rawa a fannin koyarwa.