Kungiyoyin Bokayen a jamhuriyar Nijer sun yi alkawarin yin amfani da rundunonin aljannunsu kan duk kasashen da ke yi wa Nijar zagon kasa.
Sun bayyana haka ne yayin ganawarsu da shugaban mulkin sojin kasar Abdurrahmane Tchiane a fadar Gwamnati dake yamai a jiya Alhamis.
An yi ganawar ne kan halin da Nijar ke ciki da kuma zargin da janar Abdourahamane Tiani ya yi wa wasu kasashe na bai wa Faransa hadin kai don shuka wa Nijar makarkashiya.
A yan kwankin nan ana cigaba da samun sa in sa tsakanin nijer din da makwabciyarta Najeriya, kan zargin hada kai da kasashen yamma irinsu Faransa wajen haddasa rikici a Nijer zargin gwamantin Najeriya ta musanta
Bokayen basu kama sunan kasar da suke wa barazanar ba, to sai dai shugaba Tchiani ya gode da goyan bayan da suka nuna wa gwamnatin sojin kasar a wannan lokaci da yace makiya sun sawo kasar a gaba.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga gwamnatin Najeriya ko kuma bokayen dake Najeriya kan wannan batu.