Kungiyar Malaman kwalejin Fasaha (ASUP), reshen jihar Kano, ta tsunduma yajin aikin gargadi na makonni biyu.
Kungiyar ta fara yajin aikin a ranar 2 ga Disamba, 2024 domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda gwamnatin tarayya ta ki biyan bukatunsu.
Aniyar tafiya yajin aikin na kunshe a cikin sanarwa da sakataren yada labarai na kungiyar, Babangida Sa’adu, ya sanyawa hannu, kuma aka raba ga manema labarai a Kano.
Kungiyar ta fara yajin aikin ne bayan amincewar taron kasa da ya gudana tsakanin kwalejin fasaha 112 a Abuja a ranar 28 ga Nuwamba, 2024.
Ko a baya, ASUP ta ba gwamnatin tarayya da sauran hukumomi wa’adin kwanaki 15 domin duba matsalolin da ke damun kwalejin.