Gwamnatin tarayya ta shirya kafa wani kwamitin musamman don karfafa mallakar gandun daji ga masu zaman kansu a Najeriya.
Wannan matakin na daga cikin kokarin gwamnati don yaki da sare dazuka ba tare da tsari ba, kara yawan gandun daji, da kuma inganta rawar da bangaren masu zaman kansu ke takawa wajen kula da gandun daji.
Ministan Muhalli, Balarabe Lawal Abbas, ya bayyana wannan shiri yayin wani taro tare da kungiyar masu kare gandun daji da samar gawayi a zamanamce (FCGICM), karkashin jagorancin shugabar kungiyar, Florence Omolola Idowu, a birnin Abuja.
Ministan ya bayyana cewa kwamitin zai hada wakilai daga hukumomin dake da ruwa da tsaki kamar Sashen Gandun Daji, hukumar hana kwararowar hamada (NGGW), shirin inganta Yanayi a Yankunan maau zafi (ACReSAL), da kuma Cibiyar Binciken Gandun Daji ta kasa (FRIN).
Sai kuma kungiyoyi masu ruwa da tsaki kamar FCGICM da Kungiyar Fitar da Itace ta kasa (WEA) duk za su samu wakilci a wannan kwamiti.
“Muna fuskantar manyan matsaloli dangane da gandun dazuka, kuma dole ne mu dauki matakai na gaggawa don shawo kan wannan al’amari,” inji Lawal.
Ya kara da cewa: “Kafa wannan kwamiti zai taimaka wajen wayar da kan jama’a game da mahimmancin gandun daji masu zaman kansu, wanda zai iya kara yawan kudin shiga na kasa tare da kara yawan gandun daji da kaso 25%, daidai da ka’idojin duniya.”
Ministan ya kuma jaddada bukatar samun hanyoyin samar da gawayi da ba su shafi sare itatuwa ba, la’akari da cewa gawayi na daya daga cikin muhimman hanyoyin dogaro ga al’ummomin kasar nan da dama.
Ya bayyana cewa ma’aikatar tana kan aiki wajen samar da hanyoyin kirkira don tallafa wa sabuwar Dokar Kasa kan Girki don rage dogaro da sare itatuwa.