Gwamna Hyacinth Alia na Jihar Benue ya bayar da hutun Kirsimeti na makonni biyu ga ma’aikatan gwamnati a jihar. Hutun zai fara daga Talata, 24 ga Disamba, 2024, zuwa Litinin, 6 ga Janairu, 2025.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya yi yayin jawabin Kirsimeti a fadar hwamnati da ke Makurdi.
Ya ce wannan lokaci na hutu zai bai wa ma’aikatan gwamnati damar yin tunani, nuna godiya, da kuma kusantar iyalansu yayin bikin Kirsimeti.
Alia ya yabawa jajircewar ma’aikatan jihar, yana mai cewa sun taka muhimmiyar rawa wajen cimma manufofin ci gaban jihar. Ya ce karin hutun ya nuna jajircewar gwamnatinsa wajen inganta jin dadin ma’aikata, tare da ba su lokaci don gudanar da shagulgulan Kirsimeti cikin nutsuwa.
Sai dai, gwamna ya bayyana cewa ayyuka masu muhimmanci kamar na cibiyoyin kudi, hukumomin tsaro, asibitoci, kashe gobara, da wutar lantarki za su ci gaba da gudana. An umurci hukumomin da abin ya shafa da su shirya tsare-tsaren cikin gida don tabbatar da ci gaba da bayar da ayyuka ba tare da katsewa ba.