Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a sakamakon turmutsutsin da ya faru a Cocin Holy Trinity Catholic Church da ke Maitama, Abuja, a ranar Asabar. Lamarin ya faru ne lokacin da ake raba tallafin abinci a cocin don taimaka wa mabuƙata a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
Rundunar ‘yan sandan Abuja ta tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari, tare da bayyana cewa yara huɗu sun kasance cikin waɗanda suka rasa rayukansu. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta ƙara da cewa mutum takwas sun samu raunuka, amma an sallame huɗu daga cikin waɗanda suka jikkata bayan an ba su kulawa a asibiti.
Bayanai sun nuna cewa an shirya wannan taron ne don taimakawa masu bukata, wanda ya jawo taron jama’a mai yawa, wanda daga ƙarshe ya haifar da turmutsutsin. Shaidu sun tabbatar da cewa turmutsutsin ya faru da misalin karfe 7 na safiyar Asabar.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa an ɗauki matakai don gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ake ci gaba da tantance adadin wadanda abin ya shafa.