Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta rage farashin kayan abinci a kasar nan.
Ya kuma tabbatar da cewa zai yi aiki tukuru domin rage hauhawar farashin kaya daga kashi 34.60 cikin 100 da aka samu a watan Nuwamba na shekarar 2024 zuwa kashi 15 cikin 100 a shekarar 2025.
Shugaban kasa ya bayyana hakan ne a cikin sakon sabuwar shekara da ya tura ga ‘yan Najeriya a ranar Laraba.
A cewar sa, gwamnatin sa tana nufin kara yawan samar da abinci a cikin kasar domin rage farashin kayan abinci a fadin kasar, tare da inganta samar da magunguna da kayan aikin lafiya na cikin gida.
Ya kuma yi alkawarin kara samun damar karbar lamuni ga ‘yan kasa da kuma muhimman bangarorin tattalin arziki.